Ministan kudi ya dawo Najeriya bayan ganin likita a kasar waje

Wale Edun ministan kudi na Najeriya ya dawo gida Najeriya bayan da yaje wata ziyara kasar waje.

Wani fefan bidiyo da ake yaɗawa ya nuna ministan a otal din Frazer Suites dake Abuja.

An bada rahoton cewa ya yi wata ganawar sirri da wata tawagar wakilan kasar Qatar a ranar Lahadi a otal din tare da Jumoke Oduwale ministan harkokin ciniki da masana’antu da zuba jari.

A makon da ya gabata ne wasu rahotanni suka bayyana cewa ministan na fama da rashin lafiya inda ya bar Abuja a ranar Litinin ya zuwa Lagos daga can kuma ya wuce kasar waje domin samun kulawar likitoci.

A makon ne dai  mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ta tabbatar da cewa Edun ba shi da lafiya.

More from this stream

Recomended