
Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya kara kudin litar man fetur a gidajen mansa dake sassa daban-daban na Najeriya.
A birnin tarayya Abuja da kuma Lagos,
an kara kuɗin litar mai ya zuwa ₦992 a birnin Abuja da kuma ₦955 a birnin Lagos.
Sabon karin da aka yi na nufin an samu karin ₦127 kan kowace lita a jihar Lagos kan naira 865 da ake sayarwa a baya a yayin da aka samu karin naira 65 kan kowace lita a birnin tarayya Abuja a mai makon 892 da ake sayarwa a baya.
Jaridar The Cable ta ziyarci gidan man NNPCL dake Ago Palace a birnin Lagos ranar Litinin inda ake sayar da man akan sabon farashin ₦992.