Sojoji Sun Daƙile Wani Harin ’Yan Bindiga a Katsina, Sun Ceto Wata Ɗaliba Ƴar Shekaru 15

Sojojin rundunar Najeriya tare da hadin gwiwar ’yan sanda sun yi nasarar dakile harin da wasu ’yan bindiga suka kai kauyen Soro Daya da ke karamar hukumar Kankia a jihar Katsina.

Rahoton masanin tsaro, Zagazola Makama, ya nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:15 na tsakar dare a ranar 19 ga Satumba, lokacin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kutsa cikin garin.

Bayan samun labari, dakarun sun garzaya wurin inda suka yi artabu mai zafi da maharan a kan hanyar Soro Daya. A yayin musayar wuta, maharan sun lalata tayar gaba da gilasan gefe na motar sulke ta ’yan sanda, kafin daga bisani su tsere cikin daji.

An ceto wata yarinya ’yar shekara 15 mai suna Nabiha Mani, wacce ta samu raunin harbin bindiga a cinyarta. An fara kai ta Asibitin Kiwon Lafiya na Matazu, daga bisani aka tura ta Asibitin Kashi na Katsina domin ci gaba da samun kulawa.

More from this stream

Recomended