Wani Abun Fashewa Ya Jikkata Dalibai Bakwai A Wata Makaranta A Benue

Dalibai bakwai na makarantar LGEA Primary School da ke Ater, karamar hukumar Ukum a jihar Benue, sun jikkata bayan wani abu ya fashe a cikin aji.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne ranar Talata, lokacin da daliban suka tarar da wani abu, suka dauka abin wasa ne, sai ya fashe.

Wani mazauni mai suna Ternenger ya ce: “Yaran sun dauki wani abu suna wasa da shi, suka saka shi cikin wani abu mai iya fashewa, sai ya tashi. Ba a rasa rai ba, amma dalibai bakwai sun ji rauni. Wannan ba harin makamai bane, hatsari ne kawai. Kuma bangaren makarantar ya lalace.”

An ce abubuwan fashewar na iya kasancewa ragowar na’urorin tsaro da aka bari a baya.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da lamarin, ya ce tawagar masu kula da abubuwan fashewa ta je wajen domin bincike.

Kwamishiniyar Ilimi, Dr. Margaret Adamu, ta kai ziyara tare da tawaga zuwa makarantar da kuma asibitin St. Anthony’s Hospital da ke Zaki-Biam inda ake kula da yaran. Ta yaba da saurin matakin shugaban karamar hukumar Ukum, Jonathan Modi, tare da gode wa ma’aikatan asibiti.

Shugabar asibitin, Rev. Sr. Susan Tonguve, ta ce duk yaran sun samu kulawa, sai daya da ke bukatar karin magani na musamman a ido.

A madadin iyaye, Mzungwega Yongo ya gode wa gwamnatin jihar bisa kulawa da taimakon da ta bayar.

More from this stream

Recomended