
Sojojin Najeriya hudu sun samu raunuka a wani hatsarin mota da su ka yi a Tsaunin Mambila dake jihar Taraba.
Hatsarin ya faru ne a ranar Alhamis ayayin da sojoji suke tafiya a yankin dake da wuyar sha’ani ta fannin zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro ya bayyana.
Makama ya fadi cewa mai martaba Sarkin Mambila, Dr Shehu Audu Baju na daga cikin mutanen da suka taimaka wajen aikin ceton sojojin domin tabbatar da an basu kulawar da ta kamata.
Bayan samun nasarar ceto dakarun sojan an garzaya da waɗanda suka jikkata Barikin Bataliya ta 20 dake Serti domin samun kulawar jami’an kiwon lafiya.
Shugabannin al’umma da kuma sarakunan gargajiya dake yankin sun nuna alhinin su kan hatsarin tare da yin addu’ar samun lafiya.