Gwamnatin Imo za ta fara biyan ₦104,000 a matsayin mafi karancin albashi

Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo ya amince a fara biyan ma’aikatan jihar naira 104,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Da yake magana a wurin wani taro da kungiyoyin kwadago dake jihar ranar Talata da daddare a gidan gwamnatin jihar dake Owerri, Uzodinma ya sanar da cewa an kara mafi karancin albashi daga naira dubu 74,000 ya zuwa ₦104,000.

Ya kuma ce an kara mafi karancin albashi  likitoci daga ₦215,000 ya zuwa ₦503,000 a yayin da na malaman makarantun gaba da sakandare aka karashi daga ₦119,000 ya zuwa ₦222,000.

Gwamnan ya ce jihar Imo ta fuskanci kalubale iri-iri tun lokacin da gwamnatinsa ta kama aiki  kama da daga annobar COVID 19, matsin tattalin arziki sakamakon sauye-sauye da kuma rikici kan mafi karancin albashi da kuma cire tallafin man fetur.

More from this stream

Recomended