Fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun tsallake rijiya da baya

Fasinjoji da dama ne suka tsallake rijiya da baya  bayan da jirgin kasa da suke ciki ya yi hatsari.

Lamarin ya faru ne a kusa da garin Jere a lokacin jirgin yake kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna amma ya kauce daga kan digarsa ya fadi kasa.

Wasu hotuna da kuma fefen bidiyo da wasu daga cikin fasinjojin suka wallafa a soshiyal midiya ya nuna yadda taragon jirgin ya kife kasa a yayin da fasinjoji ke tsaye a gefen jirgin a cikin daji.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an tura dakarun soja ya zuwa wurin domin bawa fasinjojin kariya.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomi kan faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended