Yara 14 da aka sace daga Adamawa aka sayar da su a Anambra sun koma wajen iyayensu

Yan uwa da kuma iyaye sun zubar da hawayen farin ciki da kuma alhini lokacin da aka sada su da yaransu da aka samu nasarar kwato su daga jihar Anambra bayan da wasu mutane suka sace su suka sayar da su.

An mika yaran a hukumance a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Laraba da ya samu halartar mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa George Farauta inda ta ce jihar ta shiga taswirar mummunan masifar nan ta safarar yara da ta addabi ƙasarnan.

“An mayar da yaran tamkar wata hajar sayarwa. Inda ake sayar da su kan kuÉ—i tsakanin dubu 800 ya zuwa miliyan 1.7 kowannensu,”

Ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar kama wata mata mai suna, Ngozi Abdulwahab shugabar masu safarar wacce take da wani shagon sayar da kayan amfanin yau da kullum dake mazabar Jambutu a Yola North inda ta ke jan hankalin yaran da kayan kalaci daga nan ta yi safararsu zuwa yankin kudu maso gabas.

” Na zata yata ta mutu tsawon watanni biyu banyi bacci ba,” a cewar Hussaini Shehu mahaifin Fatima mai shekaru 9 wacce aka sace ta lokacin da take wasa a kofar gidansu dake Mubi North.

” Da na ganta yau ni kai na na yi kuka kamar yaro. Babu iyayen da ya kama a ce  sun shiga irin wannan kuncin,”

Aisha Isa mahaifiyar Muhammad Buba da kyar take iya magana a yayin da take rungume da É—anta.

“Sun sacen da na kwalli É—aya da nake da shi. Ina rokon Allah kullum ya dawo mun da shi. Yau na san Allah ba ya barci,” ta fada cikin rada.

More from this stream

Recomended