Mutane 7 sun yi hatsarin mota a kan titin Damaturu-Maiduguri

Mutane 7 aka tabbatar da sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru akan babban titin Maiduguri zuwa Damturu a jihar Yobe.

A cewar wani shedar gani da ido hatsarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da wata motar haya dake kan hanyar zuwa Maiduguri ta kwace daga hannun direbanta inda ta rika tuntsurawa.

Fasinjoji da dama aka bada rahoton sun samu raunuka iri daban-daban a hatsarin.

Mazauna wurin da abun ya faru sun garzaya inda suka taimaka wajen kwashe mutane zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwar 7 daga ciki.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi wadanda suka jikkata na cigaba da samun kulawa a asibiti a yayin da wasu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

More from this stream

Recomended