
Musa Gude, mamba dake wakiltar al’ummar mazabar Uke da Karshi a majalisar dokokin jihar Nasarawa ya ce ya nada mutane 106 muƙami domin su taimaka masa wajen gudanar da aikinsa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, Gude wanda aka zaba a karkashin jam’iyar SDP ya fadi haka ne a lokacin da ake tattaunawa da shi a Lafia babban birnin jihar a ranar Talata.
Ya ce ya nada muƙamin ne ba kawai don inganta yadda ake gudanar da aiki ba
a’a har ma da inganta rayuwar wadanda aka naɗa da kuma iyalansu.
“Ina so na bayyana cewa ina da masu taimaka min 106 da nake biyansu albashi.Wasunsu ana biyansu kama daga dubu ₦100,000, ₦ 80000, ₦50000, ₦30,000, ₦20000, da kuma ₦10,000,” ya ce
Dan majalisar ya kuma bayyana irin kokarin da yake wajen biyawa ɗalibai kuɗin jarabawar kammala sakandare da kuma samar da rijiyoyin burtsatse.