
Rundunar yan sandan jihar Borno ta ce jami’an ta sun samu nasarar gano wani bom da bai fashe ba a wata gona dake karamar hukumar Dikwa ta jihar.
A wata sanarwa ranar Litinin, Nahum Daso mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce jami’an sun gano bom din ne bayan da wani mutum mai suna, Babagana Kachalla ya gano wani abu da bai aminta da shi ba a gonarsa.
Daso ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Naziru Abdulamjid ya tura jami’an da suke kwance bom ya zuwa wurin.
“Samun labari ke da wuya kwamishinan yan sandan jihar Borno, CP Naziru Abdulamjid ya gaggauta tura kwamandan sansani na 13 na yan sandan dake kwance bom tare da mutanensa ya zuwa wajen,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa an samu nasarar kwance bom din mai tsayin mita mita 2.2 lami lafiya.