Mamakon ruwan sama ya lalata sama da gidaje 50 da makarantu a jihar Plateau

Akalla gidaje 50, makarantu da kuma wurin ibada ne suka lalace sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka yi a unguwar Menkaat a gundumar Shimankar dake karamar hukumar Shendam ta jihar Filato.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa ruwan saman ya yi barna sosai a yayin da turakun wutar lantarki da bishiyu suka rika fadawa kan gidajen mutane.

Bayanan da wakilin jaridar Daily Trust ya tattara sun bayyana cewa iskar mai karfin gaske da ta biyo bayan ruwan sama ta fara ne da tsakar daren ranar Lahadi.

A yayin da rufun wasu gidajen ya yaye wasu gidajen rushewa su ka yi baki daya.

Mazawaje Daniel kansilan mazabar Shimankar ya fadawa jaridar cewa  ambaliyar ruwa da kuma turbaya sun lalata amfani gona da kuma shinkafa.

Shima Mista Lawrence Longwalk mazaunin unguwar ya koka kan irin barnar da aka samu inda ya ce akwai bukatar hukumomin da abun ya shafa su kawo musu dauki.

More from this stream

Recomended