Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar kwastam Bashir Adeniyi da shekara 1

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar kwastam ta Najeriya, Bashir Adeniyi  da shekara guda.

A wata sanarwa mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya ce tsawaita wa’adin zai bawa Adeniyi damar kammala wasu sauye-sauye da yake aiwatarwa a hukumar.

Shugaba Tinubu ya nada Adeniyi a matsayin shugaban hukumar ta kwastam a watan Yunin shekarar 2023. Ya kuma tabbatar da nadinsa a watan Oktoba na shekarar.

Wa’adin jagorancinsa zai kare ne ranar 31 ga watan Agusta 2025.

Sanarwar ta bayyana  zamanantar da aikin hukumar ta kwastam a matsayin daya daga cikin ayyukan da shugaban zai kammala.

More from this stream

Recomended