
Dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai dake yaki da mayakan ISWAP da Boko Haram a yankin arewa maso gabasĀ sun kashe mayakan Boko Haram guda biyu tare da gano wasu kayayyakin ta’addanci a yayin wani harin kwanton bauna da su ka yi wa mayakan a kauyen Bula Daburu dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce harin wani bangare ne na Operation Desert Sanity da aka tsara kai wa domin ruguza yadda yan ta’addar suke safarar makamai da kayayyaki.
Wata majiyar jami’an tsaro ta bayyana cewa an kai harin ne a ranar Litinin da misalin karfe 06:00 na yamma a wata hanya da a ke zargin mayakan na Boko Haram su na kai komo ta wurin.
Dakarun sun tilastawa yan ta’addar ranta a na kare sakamakon ruwan wuta inda sukaĀ tsere cikin daji tare da barin kayan da su ka dauko.
Yan ta’adda biyu aka kashe a musayar wuta a yayin da wasu suka gudu da raunin harbin bindiga.