An Binne  Gawarwarkin Manoma 27 Da Aka Kashe A Plateau

An yi jana’izar manoma 27 da yan bindiga suka kashe a jihar Filato inda aka binne su a lokaci guda.

Mutanen da suka hada da maza da mata an kashe su ne a ranar 15 ga watan Yuli lokacin da yan bindiga suka kai hari a Bindi-Jebbu dake garin  Tahoss a karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

Maharan sun farma garin  suka rika kona gidaje, lalata amfanin gona inda suka yi mummunar barna a garuruwa takwas.

Mutane da dama sun jikkata inda suka samu kulawa a Asibitim Koyarwa na Jami’ar Jos na gwamnatin jihar Plateau.

Gwamnatin jihar Plateau ta soki rundunar soja dake aikin samar da tsaro a jihar kan yadda suka gaza maganin harin duk da cewa ya faru mitoci daga wani shingen binciken sojoji.

Da yake magana a wurin jana’izar a ranar Juma’a, Bature Shuwa shugaban karamar hukumar Riyom ya yi ta’aziya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu.

More from this stream

Recomended