
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karbi bakuncin takwarorinsa tsofaffin gwamnonin da suka yi mulki a tare a shekarar 1999 wadanda suka kawo masa ziyara a fadar Aso Rock dake Abuja.
Tinubu ya jagoranci jihar Lagos daga shekarar 1999 ya zuwa 2007 a karkashin jam’iyar AD.
Tawagar da ta kunshi gwamnonin Najeriya farar hula na farko bayan da kasar ta dawo mulkin farar hula sun samu jagorancin tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori a yayin ganawar.
Wadanda suka samu damar halartar ganawar sun hada da Adamu Aliero (Kebbi), Joshua Dariye (Plateau), Saminu Turaki (Jigawa), Boni Haruna (Adamawa), Donald Duke (Cross River) da kuma Sam Egwu (Ebonyi).
Sauran sun hada da Lucky Igbinedion (Edo), Jolly Nyame (Taraba), Victor Attah (Akwa Ibom), Niyi Adebayo (Ekiti), da kuma Adamu Mu’azu (Bauchi).
George Akume, tsohon gwamnan jihar Benue daga 1999 zuwa 2007 kuma sakataren gwamnatin tarayya shi ne ya gabatar da tsofaffin gwamnonin gabanin fara taron.
Tsofaffin gwamnonin da ba a ga keyarsu ba a wurin taron sun hada da Bisi Akande (Osun), Olusegun Osoba (Ogun), Achike Udenwa (Imo), Abdullahi Adamu (Nasarawa), Ahmed Makarfi (Kaduna), Attahiru Bafarawa (Sokoto), Sani Yerima (Zamfara), Rabiu Kwankwaso (Kano), Chimaroke Nnamani (Enugu), da Orji Kalu (Abia).