Yan sanda a Kaduna sun kama wani gawurtaccen dan bindiga

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama Mati Bagio wani gawurtaccen dan bindiga da ya shafe shekaru 11 ana nemansa ruwa a jalllo.

Mansir Hassan mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya ce an kama wanda ake zargin mai shekaru 34 a gidansa dake Unguwar Galadima a garin Shika na karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Hassan ya ce wanda aka kama din jagorancin gungun  yan ta’adda da su ka kai munanan hare-hare da dama a kananan hukumomin, Giwa, Hunkuyi, Faskari, Faskari, Dandume da kuma Funtua dake jihohin Katsina da Kaduna.

Ya ce yan sanda sun samu bindiga kirar AK-47 guda daya, AK-47 kirar gida guda daya, bindingar Pump Action guda daya da kuma karamar bindiga Pistol guda biyu a tare da shi.

Sauran makaman da aka samu tare a shi sun hada da gidan harsashin bindigar Ak-47guda biyu, harsashin Pistol guda 87, hannun AK-47 kirar gida guda 10 da adda da kuma sauran kayayyaki.

“Wannan kamen wata babbar nasara ce a kokarin da muke na kawar da batagari da kuma kawar da haramtattun makamai daga cikin al’ummomin mu,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike domin kawo ragowar sauran batagarin dake taimaka masa wajen aikata barna.

More from this stream

Recomended