Wasu Yara Sun Kubuta Bayan Shafe Shekaru 5 A Hannun Boko Haram

Rundunar yan sandan jihar Borno, ta ce jami’anta sun  mayar da wasu yara biyu hannun iyayensu bayan da su ka shafe shekaru 4 a hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa ranar Talata, Nahum Daso mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar  ya ce yaran biyu Ayuba Ishaku da Yakubu Haruna dukkaninsu dake da kusan shekaru 13 sun isa hedkwatar shiyar ta rundunar yan sandan jihar ne a ranar 12 ga watan Yuli.

Daso ya ce an dauke yaran ne tare da wasu mata kananan yara a lokacin wani farmaki da mayakan su ka kai kauyen Madaragrau dake karamar hukumar Biu ta jihar Borno a shekarar 2019

Ya ce an dauke su ya zuwa Mangari da Tumbun Mota dake yankin Baga a karamar hukumar Kukawa ta jihar inda anan aka tsare su.

Mai magana da yawun rundunar ya ce yaran sun bayyana yadda aka tilasta musu zama yan aikin cikin gida tare da basu hore kan yadda ake kula da makamai..

Ya ce bayan shafe watanni suna shiri da tsari sun samu nasarar  tserewa a ranar 8 ga watan Yuli inda su ka yi amfani da damar da suka samu bayan da mafi yawa daga cikin yan bindigar su ka tafi kai wani farmaki.

“Sun bi ta cikin dazuka ya zuwa kauyuka da garuruwan dake kusa kafin su samu kansu a birnin Maiduguri a ranar 12 ga watan Yuli,” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended