
Tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ya rasu a birnin London bayan da ya shafe kwanaki yana jinya.
Mai magana da yawun tsohon shugaban kasar, Mallam Garba Shehu shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin iyalan Buhari.
” Iyali na sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari da maraicen yau a wani asibiti a London,” a cewar gajeriyar sanarwar.
Sanarwar tayi addu’ar Allah Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi.
Buhari ya shafe kwanaki yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba a birnin London.