An dakatar da shugaban jam’iyar APC na jihar Nasarawa

Shugabannin mazabar shugaban jam’iyar APC na jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello sun dakatar da shi daga jam’iyar bayan da suka zarge shi da yi mata zagon kasa.

Ibrahim Iliyasu, shugaban jam’iyar APC na mazabar Gayam dake karamar hukumar Lafia ta jihar  shi ne ya sanar da dakatarwar a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata.

Ya ce matakin da suka dauka ya samu goyon bayan dukkanin shugabannin mazabar Gayam an dauki matakin ne sakamakon saba doka ta  21 ta kundin tsarin mulkin jam’iyar APC da shugaban ya yi.

Ya zargi Bello da goyawa dantakarar jam’iyar adawa  da kuma yi masa  yakin neman zabe a fili karara.

A cewar shugaban mazabar dakatarwar ta fara aiki nan take inda suka shawarci Bello da ya daina ayyana kansa a matsayin mamba a jam’iyar APC a mazabar Gayam.

More from this stream

Recomended