Gobara ta kone gidan biredi a Zuba

Gobara ta kone wani gidan biredi dake kallon babban Masallacin Juma’a dake Zuba yankin Gwagwalada a birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin yankin, Shuaibu Abdullahi ya fadawa jaridar Daily Trust cewa gobarar ta kama ne da karfe 04:20 na  maraicen ranar Alhamis

Ya ce gobarar wacce kawo yanzu ba a san musabbabin ta kone baki dayan gidan biredin duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba a gobarar.

Ya ce ”  Babu wutar lantarki a lokacin da wutar ta fara ci. Daya daga cikin ma’aikatan ne ya ga hayaki ya turnuke yana tashi daga cikin rufi shi ne ya ankarar da mutane.”

Gobarar ta kama ne dai-dai lokacin da ma’aikata suke tsaka da yin aiki.

Jami’an kashe gobara daga garin Tungar Maje dake da tazarar kilomita 1 daga  Zuba sun isa wurin domin kashe wutar duk da cewa wutar ta kama baki dayan wurin.

More from this stream

Recomended