
Wata motar tanka ta kama da wuta a lokacin da take sauke man da ta dauko a wani gidan mai dake kan titin Old Akure a Obawole a jihar Lagos.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta fara ne a wani gini dake bayan gidan man da karfe shida na yammacin ranar Laraba.
Hukumar kashe gobara ta jihar Lagos ta tabbatar da faruwar gobarar kuma ta kuma tabbatar da cewa babu ko da mutum daya da ya rasa ransa ko ya jikkata.
A cewar Jibril Gawat mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya ce an samu nasarar kashe gobarar inda ya kara da cewa ana cigaba da aiki domin killace wurin.
Gawat ya ce motocin kashe gobara hudu aka tura wurin daga ofisoshin kashe gobara na Agege, Ikeja da kuma Alausa.
Ya yabawa hukumar kashe gobara ta jihar Lagos kan yadda suka yi aikin shawo kan gobarar.