
Dakarun rundunar sojan Najeriya dake aiki karkashin rundunar Operation Forest Yakin(OPFY) sun samu gagarumar nasara a cigaba da yakin da su ke da yan bindiga a jihar Zamfara bayan da suka kashe gawurtaccen dan bindinga Auta da kuma wasu daga cikin yaransa a wani farmaki da suka kai masa.
A cewar wasu majoyoyin tsaro an kai farmakin ne a ranar 10 ga watan Yuni a wajejen garin Kunchin Kalgo dake karamar hukumar Tsafe ta jihar.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro dakarun sun kuma kashe yanbidiga Abdul Jamilu da kuma Salisu tare da Auta.
Sojojin sun yi musayar wuta da yan bindiga inda har su kaci karfinsu tare da kashe su.Amma kuma kawo yanzu ba a san inda dan bindinga Babaye a wasu na kusa shi suka shiga ba bayan fadansu da sojojin amma kuma mazauna yankin na cewa akwai yiyuwar shima an kashe shi a musayar wuta.