Musulman Abia Sun Yi Bikin Sallah Inda Suka  Yi Addu’ar Samun Zaman Lafiya da Tattalin Arziki Ga Najeriya

A ranar Juma’a, Musulman jihar Abia sun taru a filin wasan Umuahia domin gudanar da sallar Eid al-Kabir tare da sauran Musulmi a fadin duniya.

Sallar ta fara da misalin karfe tara na safe inda dimbin mabiya addinin Musulunci suka halarta cikin shigar bukukuwa da nishadi.

A sakonsa na Sallah, Babban Limamin Masallacin Umuahia, Alhaji Aminu Lawal, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, hadin kai da hakuri. Ya bukaci Musulmi da su nuna a zahiri ruhin wannan biki mai tsarki ta hanyar kyawawan dabi’u da zamantakewa.

Limamin ya gode wa Allah da ya basu damar ganin wannan Sallah cikin koshin lafiya, tare da bukatar a yi koyi da kyawawan halaye na Annabi Muhammad (SAW).

Ya kuma yi kira ga Musulmi da su kara zage damtse wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da farfadowar tattalin arzikin kasa, yana mai cewa halin da ake ciki na bukatar addu’a da hadin kai tsakanin kabilu da addinai.

“Muna ‘yan uwa ne gaba ɗaya,” in ji Limamin. “Mu zauna lafiya tare ba tare da bambanci ba.”

Alhaji Lawal ya yaba wa Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, bisa yadda yake ba Musulmi muhimmanci a harkokin gwamnati da kuma daukar nauyin wasu zuwa aikin Hajjin bana.

Wasu daga cikin Musulman da suka halarci sallar kamar su Sanusi Mohammed, Emeka Ibelegbu Mohammed, Alhaji Abdulkamin Adekunle da Dahiru Alhassan sun bayyana wannan rana a matsayin wata muhimmiyar ibada a Musulunci. Sun kuma gode wa Allah tare da yin kira ga jama’a da su zauna lafiya da juna.

Sallar ta kare da yanka ragon sadaukarwa da Limamin ya jagoranta domin tunawa da sadaukarwar Annabi Ibrahim da yadda Allah Ya sauya masa hadaya.

More from this stream

Recomended