
Karin gawarwarkin yara 7 aka sake zakulowa daga baraguzai kwanaki shida bayan da mummunan ambaliyar ruwa ta afkawa al’ummar garin Mokwa, hedkwatar karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.
A cewar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA an gano gawar yara guda hudu a ranar Litinin a yayin da aka gano karin wasu a ranar Talata inda hakan ya kawo yawan mutanen da suka mutu ya zuwa 160 a hukumance.
Shugaban hukumar ta NSEMA, Abdullahi Baba Arah ya ce hukumar ta dauki mazauna garin aiki domin su taimaka wajen zakulo gawarwarkin mutanen dake rubewa a cikin baraguzan gini.
Amma kuma kwamishinan ayyukan jinkai na jihar Neja Ahmad Sulaiman ya ce gawarwarkin mutane sama da 200 aka gano kawo yanzu.
Da yake magana a cikin shirin Morning Brief na gidan talabijin din Channels kwamishinan ya ce ” Babu wanda zai fada maka yawan mutane da suka mutu a jihar Neja a yanzu saboda har yanzu muna cigaba da neman wasu gawarwarkin.”