
Siminalayi Fubara, dakataccen gwamnan jihar Ribas a ranar Talata ya ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a gidansa dake Lagos.
Ziyarar na zuwa ne mako guda bayan da gwamnan ya sanar da cewa ya jingine alfahari da kuma bukatar kashin kansa domin dawo da zaman lafiya a jihar.
Amma kuma har babu wani cikakken bayani da ya fito game da abun da ganawar ta mayar da hankali akai.
Fubara ya ce zai yi sulhu tsohon mai gidansa kuma mutumin da ya gada, Nyesom Wike Wanda yake kira da “maigida”.
“Dole mu sauko da kan mu kasa daga dokin fushi da muka hau mu kuma mika kan mu ga shirin samar da zaman lafiya wannan shi ne abun da muke yi yanzu,” ya ce.
“Abu mafi muhimmanci shi ne jihar ta samu ta cigaba bukatar jihar ita ce gaba da komai,”