
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 6 ga watan Yuni da kuma ranar Litinin 9 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun bikin Babbar Salah.
Olabunmi Tunji-Ojo ministan harkokin cikin gida shi ne ya sanar da ranakun hutun a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ta hannun Magdalene Ajani babbar sakatariyar dindin ta ma’aikatar.
Ministan ya taya biki dayan musulmi murnar gabanin fara shagulgulan bikin.
“Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a 6 da kuma Litinin 9 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Babbar Sallah ta wannan shekara,” a cewar sanarwar.
“Ministan harkokin cikin gida, Dr Olabunmi Tunji-Ojo wanda ya ayyana haka a madadin gwamnatin tarayya ya taya dukkanin musulmi na gida dana kasashen waje murnar bikin,”
Ministan ya yi kira ga Al’ummar Musulmi su yi koyi da sadaukarwa da kuma imani kamar yadda Annabi Ibrahim ya yi kana su kuma yi addu’ar samun zaman lafiyar da wadata a Najeriya.