
Muhammad Abdullahi tsohon ministan muhalli a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar APC.
Karkashin gwamnatin Buhari da farko an nada Abdullah karamin ministan kimiya da fasaha kafin daga bisani a mayar da shi ma’aikatar muhalli.
Sanarwar fitarsa daga jam’iyar na kunshe ne cikin wata wasika da ya aikewa jam’iyar.
Wasikar an aiketa ga shugaban jam’iyar na mazabar Uke dake karamar Karu ta jihar Nasarawa aka kuma bada kwafinta ga sauran shugabannin jam’iyar.
Tsohon ministan ya ce ya fice daga jam’iyar bisa wasu dalilai na radin kansa.
Ya godewa shugaban jam’iyar na mazabar bisa goyon baya da kuma hadin kai da ya samu lokacin yana APC.