Mutane 25 sun mutu 10 sun bace a ambaliyar ruwa jihar Niger

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger(NSEMA) ta ce mutane 25 suka mutu a yayin da sama da 10 suka bace biyo bayan ambaliyar ruwan da ta faru a garuruwan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa dake karamar hukumar Mokwa ta jihar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, Abdullahi Arah shugaban hukumar ya ce ambaliyar ruwan ta shanye tare da yin awon gaba da gidaje sama da 50 da kuma mutanen da suke ciki.

Arah ya ce ambaliyar ruwan ta faru ne biyo bayan mamakon ruwan sama da aka dauki awanni ana yi da daren ranar Laraba.

Ya ce jami’an hukumar tare da taimakon ma’aikatan karamar hukumar, wadanda suka iya ruwa da kuma yan sakai sun samu nasarar ceto wata mata da yayanta guda biyu.

Arah ya kara da cewa ana cigaba da aikin nemo gawarwarkin sauran mutanen.

More from this stream

Recomended