Dakarun rundunar sojan Najeriya dake aiki a rundunar Operation Fansar Yamma da take yaki da yan bindiga a yankin arewa maso yamma sun samu nasarar kashe yan bindiga da dama a wata arangama da suka yi a jihar Katsina.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi dakarun sun gwabza da yan bindigar ne a kauyen Ruwan Godiya dake karamar hukumar Faskari ta jihar a ranar 23 ga watan Mayu.
Ya ce sojojin sun samu nasara akan yan bindigar ne a wata mummunan fafatawa da suka yi abun da ya tilastawa yan bindigar tserewa daga sansanin.
A lokacin da suke tserewar ne dakarun suka bi su da ruwan wuta inda suka kashe 21 daga cikin su a yayin da wasunsu suka nutse a wani kogi dake kusa.
Har ila yau sojojin sun samu nasarar kwace bindigogi da dama da kuma baburan hawa daga hannun yan bindigar.
