Sarki Sanusi ya karbi bakuncin El-Rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ziyarci mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a fadarsa dake Kano a ranar Litinin.

A yayin ziyarar El-Rufai na tare da wasu makusantansa har ya zuwa wallafa wannan labarin babu wata sanarwa da aka fitar dake bayyana makusidin ziyarar ta El-Rufai.

Ziyarar na zuwa ne dai-dai lokacin da ake cigaba da takun saka tsakanin El-Rufai da kuma gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jam’iyar APC.

More from this stream

Recomended