Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 12 a Borno

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe yan bijilante 2 da kuma wasu mutane 10 masu yin ita ce a kauyen Bokko Ghide dake karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kashe yan bijilante din ne a wani kwanton bauna da aka yi musu akan titin Kirawa dake gundumar Pulka.

Ya ce sauran wasu mutane 10 da abun ya rutsa da su sunje daji ne neman itacen girki

“Sun je dajin dake kusa neman ita ce a ranar Asabar lokacin da mayakan suka yi musu kwanton bauna suka kashe 10 daga ciki suka bar mutane biyu da mummunan rauni,” ya ce.

“Mun binne mutane 10  muka Kai wadanda suka jikkata asibiti a Maiduguri domin samun kulawar likitoci”

“Abin da ciwo biyu daga cikin Civilian JTF dina da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare mutane na suma an kashe su a ranar Juma’a,”

More from this stream

Recomended