Ƴan bindiga sun kai hari gidan su Natasha Akpoti

Ƴan bindiga sun kai farmaki gidansu Natasha Akpoti Uduaghan sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa

An kai hari gidan ne dake Obeiba-Ihima, a ƙaramar hukumar Okehi ta jihar da tsakar daren ranar Talata lokacin da aƙalla mutane uku dake ɗauke da bindigogi da adduna suka farma gidan.

A cewar Yakubu Ovanja babban jami’in tsaron sanatan maharan sun isa gidan ne da ƙarfe 01:00 na dare inda suka fara farfasa gilasan taga da sauran kayayyaki.

Biyo bayan kiran kai ɗaukin gaggawa jami’an tsaro daga Okehi sun yi gaggawar isa wurin.

Duk da cewa ba a kama kowa ba a maharan tuni aka fara gudanar  da bincike kan lamarin.

Da take tabbatar da kai harin, Natasha ta ce maharan sun yi tunanin cewa tana gari abun da yasa suka kai hari gidansu kenan.

More from this stream

Recomended