
Aƙalla matafiya 8 ne suka mutu bayan da bam ya tashi da motar da suke ciki lokacin da suke tafiya akan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno a ranar Asabar.
A cewar rundunar ƴan sandan jihar Borno lamarin da ya jikkata wasu mutane 11 ya rutsa da wata motar haya da ta nufi Maiduguri babban birnin jihar daga Damboa.
“Da misalin ƙarfe 11:45 na yau wani mummuna lamari ya faru a ƙauyen Komala dake ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno,” a cewar Nahum Daso mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar a cikin wata sanarwa da ya fitar.
“Wata mota Hummer mai rijistar namba Jigawa MMR 144 XA ta taka wani bam da ake zargin mayaƙan Boko Haram/ ISWAP da sakawa.
“Fashewar ta jawo mutuwar mutane 8 har da direban yayin da wasu 11 suka samu raunuka daban-daban. An kai waɗanda suka jikkata asibitin kwararru na musamman dake Maiduguri domin samun kulawa,”
Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya ziyarci mutanen a asibiti ya kuma bayar da umarnin kula da su kyauta.
Zulum ya kuma basu tallafin ₦50,000 ga waɗanda suka jikkata.