Gidajen mai sun ƙara kuɗin litar man fetur a Lagos

Gidajen mai a jihar Lagos sun kara kuɗin man fetur ya zuwa ₦930 akan kowace lita.

Wani binciken da jaridar The Cable ta gudanar ta gano cewa gidan mai na First Royal dake kan titin College Road a Ogba  Lagos sun ƙara kuɗin man daga ₦860 kowace lita ya zuwa ₦930.

Suma gidajen man AS Sallam da kuma MRS dake Festac sun ƙara kuɗin man da suke sayarwa daga ₦860 ya zuwa ₦930

Ƙarin farashin kuɗin man fetur ɗin na zuwa ne dai-dai lokacin da matatar man fetur ta Dangote ta dakatar da sayar da man fetur akan farashin naira biyo bayan karewa da yarjejeniyar matatar da kamfanin mai na NNPCL.

Matatar ta Dangote ta shiga wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya inda za a riƙa sayar mata da ɗanyen man fetur akan farashin naira maimakon dalar Amurka inda itama matatar zata rika sayar da tataccen mai akan farashin naira.

More from this stream

Recomended