Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo ta tabbatar wa al’ummar Musulmi cewa an dauki matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah Eid-el-Fitr.
Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa wannan mataki yana daga cikin kudurin rundunar na tabbatar da bukukuwan Sallah sun gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Ya bayyana cewa rundunar tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun shirya tsaf domin kare lafiyar dukkan mazauna jihar kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan.
Okoye ya ce an kammala shirin tsaron ne bayan wata muhimmiyar ganawa da manyan jami’an tsaro da aka gudanar a 34 Artillery Brigade, Obinze. Wadanda suka halarta sun hada da Kwamandan Brigade, Birgediya Janar IM Abass, Daraktan Hukumar DSS DD ZM Baba, Air Cdre DE Bello, Kwamandan Sojin Sama na Najeriya, Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa na Oguta, Cdre MA Alhassan, da wakilin Kwamishinan ‘Yan Sanda, da sauransu.
Ya ce taron ya mayar da hankali ne kan dabarun tabbatar da cikakken tsaro a duk fadin jihar yayin bukukuwan.
“A cikin wannan yunkuri, ‘yan sanda, sojoji, DSS, NSCDC, NDLEA, FRSC da sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da hadin gwiwar gudanar da atisayen nuna karfin tsaro domin tabbatar wa da al’umma cewa a shirye muke domin dakile duk wata barazana ga zaman lafiya,” in ji shi.
DSP Okoye ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun gudanar da atisayen sintiri na hadin gwiwa, da ayyukan bincike a wurare masu muhimmanci domin hana bata-gari yin katsalandan ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Hakazalika, jami’an ‘yan sanda an baza su a filayen sallah, wuraren ibada, wuraren shakatawa da sauran wuraren taruwar jama’a domin hana duk wata barazana ga tsaro.
“Mun umarci kwamandojin rundunonin ‘yan sanda na yankuna, DPOs da shugabannin tawagogin tsaro da su kara kaimi wajen sintiri da hana ayyukan bata-gari a yankunansu. Ba za a amince da wata gazawa ko sakaci ba,” in ji shi.
A karshe, kakakin rundunar ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da bin doka, su kasance masu lura da tsaro tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro. Ya kuma bukaci su rika kai rahoton duk wata alama ta barazana ga tsaro zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta hanyar layukan gaggawa na rundunar.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Aboki Danjuma, yana mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi na bikin Sallah mai cike da kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Rundunar ‘Yan Sandan Imo Ta Bada Tabbacin Tsaro Ga Al’ummar Musulmi a Bukukuwan Sallah
