Wata babbar kotu a Jihar Filato ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum biyu, Thomas Danboyi da Pam Lang, saboda kashe wani mutum mai suna Chung Bot.
Babban alkalin jihar, Justice David Gwong Mann, ne ya yanke hukuncin a kotun da ke Jos a ranar Laraba, inda ya same su da laifin hada kai da kuma kisan kai.
A cewar lauyoyin da ke gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Babban Lauyan Jihar Filato, P.A. Daffi, lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Afrilu, 2010, a ƙauyen Tahai Gyel Bukuru, da ke cikin ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Bincike ya nuna cewa lokacin da marigayin da iyalansa suka je gona, mutanen da aka yanke wa hukunci tare da wasu da ba a kama ba sun kai musu farmaki.
A yayin harin, Thomas Danboyi ya rik’e marigayin, yayin da Pam Lang ya buge shi da sanda a kansa har ya suma. Daga bisani aka garzaya da shi asibitin Filato da ke Jos, inda ya rasu yana karɓar magani.