PDP Ta Sake Ɗage Babban Taron NEC Zuwa Mayu 15, 2025

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta sake ɗage babban taronta na kasa (NEC) zuwa ranar 15 ga Mayu, 2025.

Sanarwar hakan na kunshe cikin wata takarda da jam’iyyar ta fitar, wadda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye, ya sanya wa hannu.

A baya, PDP ta tsara gudanar da taron a ranar 13 ga Maris, amma aka dage shi sakamakon zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a wasu jihohi da yankuna.

Tun shekarar da ta gabata aka tsara gudanar da taron na 98, amma an ci gaba da dage shi, lamarin da ake kyautata zaton na da nasaba da wasu matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta.

More from this stream

Recomended