
Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Abia sun gano gawar mutane uku ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da aka kashe biyo bayan mummunan farmakin da aka kai a garin Azumoni Ndoki dake ƙaramar hukumar Ukwa east ta jihar Abia.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya jiwo daga wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri cewa mutanen na daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a ranar 4 ga watan Maris lokacin da wasu ƴan bindiga a cikin mota ƙirar Sienna suka kai harin kwanton ɓauna kan yan rakiyar wani ɗan kasuwa, Obasi Lawson.
Ya ce maharan sun kashe direban motar da kuma wani fasinja kafin daga bisani su tsere da ɗan kasuwar da kuma ɗaya daga cikin ƴan sandan dake bashi kariya..
Makama ya ce bayan ƴan sanda sun ɗauki tsawon kwanaki suna nema a ranar 8 ga watan Maris sun gano gawar mutane biyu wanda daga bisani aka tabbatar gawar direban ce da kuma fasinjan.
Ya ƙara da cewa bayan da aka fadada bincike an gano gawar ASP Tanko Nandip a wani daji dake kusa.
Kawo yanzu dai ba a san inda ɗan kasuwar yake ba amma jami’an tsaro na cigaba da faɗaɗa bincike.