
Jam’iyar APC a jihar Kebbi ta kaddamar da yaƙin sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma gwamnan jihar Nasiru Idris gabanin zaɓen shekarar 2027.
A wani babban taron gangamin siyasa da aka yiwa laƙabi da ” Muna bayan Tinubu da Kauran Gwandu” da ya gudana a babban birnin filin wasa na birnin Kebbi da ya samu halartar fitattun mutane ciki har da ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu, gwamna Nasiru Idris, James Faleke da kuma ƙaramin ministan ma’aikatar ilimi, Yusuf Tanko Sununu.
Da yake jawabi a wurin taron, Bagudu yace da Tinubu da Nasir Idris sun cancanta a sake zabensu a zango na biyu duba da irin ƙokarin da suka yi a cikin ƙasa da shekaru biyu da suka yi akan mulki.
Bagudu ya sanar da da bada gudunmawar miliyan ₦450 domin sayen kayan abinci a mazabun jihar 225 domin rabawa a lokacin a azumi.
A nasa jawabin gwamna Nasiru Idris ya jaddada goyon bayan da jihar take bawa shugaban ƙasa Tinubu inda ya yabawa gwamnatinsa kan gudunmawar da take bayarwa wajen cigaban jihar Kebbi.