
Aƙalla mutane biyu aka harbe har lahira a yayin da waɗanda basu gaza 10 ba aka bada rahoton ƴan fashi daji sun yi garkuwa da su a ƙananan hukumomin Wushishi da Rafi dake jihar Niger.
Wata majiyar jami’an tsaro da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana cewa mutane biyun da aka kashe ɗanbijilante ne da kuma mai yin itace.
” A yanzu haka ƴan bindiga suna Dajin Akare an yi garkuwa da ɗaya daga cikin ƴan bijilante.Lokacin da suka tafi da shi a akwai bindiga biyu a tare da shi. Bamu san me za suyi masa ba. Tun jiya(Talata) muke gumurzu da su an kashe daya daga ƴan bijilante da kuma wani mai zuwa daji yin itace,” ya ce.
Har ya zuwa karfe 05:00 na ranar Laraba mazauna garin sun bayyana cewa ƴan fashin dajin masu yawa suna Dajin Akara inda suka sace gomman shanu daga yankunan dake kewaye da su.
Kwamshinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Birgediya Janar, Bello Abdullahi Muhammad mai ritaya ya tabbatar da faruwar lamarin.