An kashe mutane shida tare da jikkata wasu da dama a rikicin siyasar Osun

Rundunar ƴan sanda a jihar Osun ta ce mutane shida aka kashe a rikicin siyasar da ya faru  a sakatariyar ƙananan hukumomin jihar a ranar Litinin.

Da take magana a cikin wani fefan bidiyo mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Yemisi Opalola ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro ya zuwa jihar domin dawo da doka da oda.

Opalola ta gargadi mutanen jihar da cewa yan sanda baza su zuba ido ba masu tayar da rikici su jefa jihar cikin rashin doka da oda.

Ta ƙara da cewa za a gudanar da bincike domin gano waɗanda suka haddasa rikicin tare da tabbatar da cewa anyi adalci.

“Rikici ya jawo asarar rayukan mutane shida tare da jikkata wasu da dama mun gode Allah  suna can suna murmurewa a asibiti,” ta ce..

” Rundunar ƴan sanda bata farin ciki da abun da ya faru jiya.”

Rikicin siyasa ya barke a jihar ta Osun bayan da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin da aka sauke suka yi ƙokarin komawa bakin aikinsu abun da ya haifar da tashin hankali.

More from this stream

Recomended