
Rikici ya ɓarke a garin Ifon hedkwatar ƙaramar hukumar Ose ta jihar Ondo a yayin da wasu fusatattun matasa suka ƙona ofishin ƴan sanda na garin.
Kawo yanzu dai babu wata majiya daga hukumomi da ta bayyana dalilin wannan aika-aika da matasan suka yi.
Wata majiya dake garin ta bayyana cewa jami’an ƴan sanda ne suka kama wani matashi inda suka azabtar da shi abun da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
A cewar majiyar hakan ne yasa matasan garin suka harzuƙa suka gudanar da zanga-zanga ya zuwa ofishin ƴan sandan har ta kai sun fatattake su tare da bunkawa ofishin wuta.
A cewar wata majiya wasu matasa ne suka yi faɗa a ranar Valentine ɗaya tsagin da aka yi rikicin da su ne suka kai ƙara ofishin ƴan sandan inda aka kama mutane biyu aka kuma azabtar da su har ta kai ga ɗaya daga cikinsu ya mutu.
Ya ƙara da cewa hakan ya fusata ƴan uwan matashin inda suka je suka ƙona gidansu wanda ya kai ƙarar tare da wucewa su ƙona ofishin ƴan sandan.