
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kashe wasu mutane biyar da ake zargin mayaƙan ƙungiyar IPOB ne dake fafutukar kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabas.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Muyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya ya ce an kai farmakin hadin gwiwa ne na jami’an tsaro kan sansanin ƴan kungiyar.
Adejobi ya ce yayin farmakin an kashe ƴan kungiyar guda biyu tare da gano bindiga ƙirar AK-47 guda biyar da kuma wasu bindigogi guda 13 da kuma tarin harsashi.
Ya ƙara da cewa a ranar 9 ga watan Fabrairu jami’an sun sake kai wani farmakin Dajin Nkwuko dake ƙaramar hukumar Mbaitoli da ya haɗa iyaka da Dajin Ubachima a Awomama a ƙaramar hukumar Oru West duk a jihar Imo inda aka kashe karin wasu mayaƙan uku.
Har ila yau jami’an tsaron sun gano bindigar AK-47 guda biyu dake ɗauke da harsashi 31 da kuma bindigar dobul barel guda ɗaya adduna da kuma baburan hawa guda huɗu