2027: ‘Yan Najeriya Za Su Kada Kuri’a Ga APC Daga Sama Har Kasa – Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa a babban zaben 2027, masu kada kuri’a za su zabi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) “daga sama har kasa.”

Gwamnan ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar yayin gagarumin taron jam’iyyar da aka gudanar a Murtala Square, inda jiga-jigan siyasa 50 suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.

A cewarsa, shaharar jam’iyyar da karbuwarta a tsakanin jama’a na da nasaba da adalcin shugabancinta a matakin jiha da tarayya.

Uba Sani ya kara da cewa APC ta kafu sosai a Kaduna, Arewa baki daya, da ma kasa gaba daya.

“A zaben 2027, jama’a za su kada kuri’a ga APC a dukkan zabuka daga sama har kasa.

“A sama, shugabanmu, Bola Ahmed Tinubu, za a sake zabarsa.

“A matakin jiha, jam’iyya za ta lashe zaben gwamna, Majalisar Tarayya da Majalisar Jiha, da yardar Allah,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa masu sauya sheka cewa za su sami kima da damarmaki iri daya da sauran mambobin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa APC jam’iyya daya ce kuma za ta ci gaba da kasancewa daya har bayan 2027.

A cewarsa, babu bambanci tsakanin wanda ya shigo jam’iyyar yau da wanda ya kasance cikinta tun shekaru goma da suka gabata.

Ya ce: “Wanda ya shiga APC yau da wanda ya kafa ta shekaru goma da suka wuce, duk suna da matsayi daya. Za su samu dama da hakkoki iri daya.”

More from this stream

Recomended