Kamfanin NNPCL ya rage farashin mai a Lagos

Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya rage farashin man fetur a gidajen mansa dake Lagos.

A cewar jaridar The Cable ta lura cewa gidajen man kamfanin dake kan titin Idimu sun rage farashin daga ₦960 ya zuwa ₦940 kan kowace lita.

Har ila yau a gidajen man kamfanin dake kan titin Ago Palace, Okota ana sayar da lita guda akan ₦945.

Rage farashin da kamfanin ya yi na zuwa ne ƙasa da makonni uku bayan da kamfanin ya sanar da karin kuɗin man fetur daga ₦925 ya zuwa 960 a gidajen man kamfanin dake Lagos.

Amma kuma farashin man fetur ɗin a gidajen kamfanin na NNPCL dake Abuja yana nan yadda yake bai canza ba .

More from this stream

Recomended