Babban Layin Lantarki na Najeriya Ya Sake Samun Matsala

Babban layin wutar lantarki na Najeriya ya fuskanci wata matsala, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a wasu sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safe.

Sai dai kamfanin ya tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki na aiki tuƙuru don dawo da wutar da zarar an magance matsalar.

Babban layin lantarki na Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin faɗuwa, musamman a shekarar da ta gabata, abin da ke haddasa yawaitar katsewar wuta a faɗin ƙasar.

More from this stream

Recomended