Dokar haraji ta tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai

Kudirin dokar haraji da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gabatarwa da majalisar ƙasa ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai ta tarayya.

A cikin watan Oktoba, Tinubu ya shawarci majalisar da zartar da kudirin dokar harajin.

Da yake jagorantar tattaunawa kan dokar a ranar Laraba, Julius  Ihonvbere shugaban masu rinjaye na majalisar ya ce an samar da dokokin harajin domin sauya dokokin haraji da aka daɗe ana amfani da su.

Ya tabbatarwa da jama’a gyaran zai amfani talakawa ƴan Najeriya ba tare da ƙara ɗora musu wani nauyin harajin ba.

Batun gyaran dokar harajin batu ne da jawo ce-ce-kuce musamman daga shugabanni da al’umma da suka fito daga yankin arewa.

More from this stream

Recomended