Dakarun Najeriya Sun Daƙile Wani Yunƙuri Na Satar Mutane, Sun Kuma Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa da Su a Plateau

Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun samu nasarar hana wani yunkurin sace mutane tare da ceto wasu mutum uku a kan hanyar Barkin Ladi zuwa Mangu, a kauyen Mairana da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau.

An gudanar da wannan samame ne a ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2025, bayan samun sahihan bayanai kan lamarin.

Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

A cewarsa, an yi garkuwa da mutanen ne da misalin karfe 7:45 na safiyar ranar 11 ga Fabrairu.

Bayan haka, dakarun Sashen 8 na Operation Golden Peace suka gaggauta isa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da wata mota kirar Ford Space Bus mai launin ja a gefe.

A cewar Makama, “Dakarun sun kaddamar da bincike a dazukan da ke kusa da wurin, wanda hakan ya kai ga nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani rauni ba.”

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun tsere bayan sun hango isowar jami’an tsaro.

Daga bisani, an maido da wadanda aka ceto ga motarsu, inda suka ci gaba da tafiyarsu cikin koshin lafiya.

More from this stream

Recomended