Mutane 30 aka tabbatar sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru a Onipetsi dake kan babbar hanyar Ore-Lagos a jihar Ondo.
Hukumar FRSC dake kare afkuwar hatsura akan titunan Najeriya ita tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi.
Samuel Ibitoye kwamandan shiya na hukumar a jihar Ondo ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Asabar.
Ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da wasu motocin haya guda biyu suka ci karo da juna suka kuma kama da wuta.
Ibitoye ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa ɗaya daga cikin motocin ce ta bi hannun da ba nata ba abun da ya kai ga sun yi tawo mu gama.
Ya ƙara da cewa mutane 28 ne suka ƙone ƙurmus har lahira nan take a yayin da mutane biyu suka mutu akan hanyar kai su asibiti.
Ya ce mutane biyu da suka tsira da ransu na samun kulawa a asibiti.
Kwamandan na FRSC ya bada tabbacin cewa binciken da za a gudanar zai bayar da ƙarin haske kan hatsarin.